Home ๐ŸŽฌ Bollywood ๐ŸŽต Pakistani ๐ŸŽค English Pop

Soyayyar Mu

๐Ÿ‘ค Salim Smart โ€ข ๐ŸŽผ Soyayyar Mu โ€ข โฑ๏ธ 4:03
๐ŸŽต 1375 characters
โฑ๏ธ 4:03 duration
๐Ÿ†” ID: 11552124

๐Ÿ“œ Lyrics

(Salim Smart on the beat)

Kan abinda kake so
Baka fiye ganin aibu ba
So yamin bazata yasa ina fargaba
Wasu sun ce hali sai yazo daya ake zama
Ni kuma nayi musanta hakan ina tantama
So kan canza hali koko ra'ayin mu ma
Tunda shi kadai ne ke sarrafa zuciya

Da so kama ne
Koko dan Adam ne
Ba zana bari ya shige mini zuciya ba
Daga kanka naga ne
So hadari ne
Kuma wajibi ne, bamu tsallake ba

Halin ka ba zai sani in guje ka ba
Addu'a nasan ba abinda bata barshi ba
Rai da zuciyata basu san wanin ka ba
Taya ido zai runtsa bai ganka ba
Inna rusuna maka, ba don niba
Duk wanda yayi sama, ka gyara hali
Zan kyautata maka, in da dada
Komai inyi maka, ba gajiya

Akan son ka duba yanda nabar hayyaci na
Bani gane komai, a dare ko Kuma da rana
Ba zana bari ba, koda zan rasa raina
A cutar da kai, hakan shine kudiri na
Taimaka min na samo sukuni
Zuciyata ko ta daina rauni
Tallafa min, kokwanto ya barni
Inji dadin zaman duniya

Koba don niba, da akwai yan uwa
Ko babu su, kasan akwai mutuwa
Ga kwanaki suna sake raguwa
Ga shekaru suna kara hauhawa

Kowanne dan Adam akwai kaddaran shi
Kowanne so da akwai silar faruwar shi
Duk wata zuciya tana dauke da tabon shi
Nima tawa duba akwai irin shi
Ko kiso, ko kar kiso naki ne ni
A zuciyar ki, babu kowa kamar ni
Tunda so har ya shigo tsakani
Kibar tunanin zani canza hali
Ko mutuwa, bata raba mu ga misali
In babu ke, ya zan yi rayuwa?

โญ Rate These Lyrics

โ˜†โ˜†โ˜†โ˜†โ˜†
Average: 0.0/5 โ€ข 0 ratings